1) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata. Ba wani iko ko'ina sai naka, Sarkina. Kai yaro ne a da tare da mu ka sha Jaraba, kai Mai Nasara, Yesu Mai Cetona. 2) Yesu, na naɗa ka a cikin zuciyata. Ba wani wanda na ke so shi amshi mulkinta Da zunubi kaɗai ya cika nawa rai, Amma yanzu na sani kai Ubangijina ne. 3) Yesu, na naɗa ka, ban rage kome ba, A bisa nawa duk da ni, sarauta za ka yi. Da goshinka ya sha azabar naɗin ƙaya, Yanzu ka ratsa mutuwa, ya kai Mai Nasara! 4) Yesu, an naɗa ka domin biyayyarka. Suna mafifici aka ba mai mulkin mutuwa. Yesu, ka cancanci ƙauna madauwamiya. An naɗa ka! An naɗa ka tun da har abada! 5) Allah ya naɗa ka Ɗansa Maɗaukaki. Baki ya kasa furtawa labarin girmanka. Gare ka ɗaukaka har abada, Amin An naɗa ka! An naɗa ka! Immanuel Almasihu.Сесини Дуялим ᠳᠣᠷᠣᠢ ᠪᠠᠶᠢᠬᠤ ᠳᠤ ᠮᠢᠨᠢ Lo zelo suo yạ mlyk ạlmjd fy mlʾ ạlzmạn Добрый Добрый Отец 复兴的火 El Shaddai kạn fy ạlbstạn Przez różnych ziem krainy Ons is almal her te saam
Song not available - connect to internet to try again?