1) Yesu Ubangijinmu, ga mu nan a gabanka. Kai ka kawo dukanmu yinin nan da lafiya Muna rera waƙarmu, muna maka godiya. 2) In yau wata jaraba za ta kai mu haɗari, Ba mu ikon jurewa, ƙara mana ƙarfi kuwa, Kiyaye mu lafiya, har mu ka da zunubi. 3) Bisa ga maganarka, daidaita rayukanmu, Bishe mu da Ruhunka, amshi mulkin nufinmu. Bar mu miƙa gare ka hadaya ta zuciyarmu. 4) Ji yanzu addu'armu, ji mu, muna roƙonka. Da mu duk da ƴanuwa, baiwarka mafificiya Ita ce bukatarmu, sahihiyar zuciya. 5) Haka za mu bayyana yau da gobe godiyarmu. Haka za mu ɗaukaka sunan Ubangijinmu. Za mu shaida yabonka, Almasihu Allahnmu.Jésus, tu es ici A Dieu soit la gloire Králi na Nebesích Menjetek be kapuin A ti nos llegamos kl ʿạm Track 5 Сəнин ишлəрин чох мөҹүзəлидир ạ̉nt hw ạlrb wḥdk LORD, I'M COMING HOME
Song not available - connect to internet to try again?