1) Yesu ya cece ni, za ya taya ni. Muddar ya riKe ni, tsoro ba na ji. Shi amintacce ne, sai in dogara, Duk alkawaransa za ya aikata. 2) Yesu ya same ni, huntu, ƃatacce. Ina so in ji shi, kullum shi kaɗai. Sa'ad da ya kira, amsa za mu yi, Ko'ina ya nufa sai mu riƙa bi. 3) Yesu Makiyayi, shi ya ba da rai Kada tumakinsa duk su lalace. Ubansa mai ƙauna yana riƙonmu, Daga hannuwansa ba mai fizgewa. 4) Yesu Makiyayi, shi ne ƙofar rai, Masu Bi sun shiga dukansu sosai. Sa'ad da zai komo, za ya tattara Dukanmu gabansa, ma ga fuskarsa.Qudaı meni jaratty Salmo 27 Tashi, Mu Gai da Ubangijinmu Гювен Яврум Агар ман тарсам Zi de zi Isuse drag My legie jsme z Nazareta Come Behold the Wondrous Mystery Non potrò ripagarti Сен Бюйюксюн
Song not available - connect to internet to try again?