1) Yesu yana bakin ƙofa, Yana ta da murya, Ku ƴan Adam duk, ku ji ni, Shiga ƙofar hanyata. 2) Ƙofan nan da wuyar shiga Hanya kuwa ƙunƙunta ce, Masu shiga babu yawa, Sai mutane kima ne. 3) Dukan masu son adalci, Dukan masu ƃacin rai, Masu ladabi a ruhu, Su ke shiga, su kaɗai. 4) Ba da dukiya za mu je ba, Ba kuwa da aniya ba, Ba don aikin nagarta ba, Sai da bangaskiya kaɗai. 5) Wata ƙofa tana nan kuwa, Masu shiga sun yi yawa, Hanyan nan kuwa ke da fādi Za ta kai su halaka. 6) Hanyan nan da sauƙi ta ke, Gama babu kokawa Da jaraba ko mugunta, Ba kuwa masu hanawa. 7) Ba su ganin inda za su, Ba tsammanin halaka. Duniya duk da ruɗin Shaiɗan Su kan rufe idonsu. 8) Tashi, masu laifi duka, Sai ku nemi gafara, Sai ku karƃi kyautar Allah Sai ku riƙa yin godiya.C'è poco cielo Kto Božej vôli poddáva sa Я желаю быть с Тобой Христос кто познал Твое имя здесь Tu vezi că lacrimi ne brăzdează faţa Возрадуйся душа моя mhwb msẖ rạḥ ạ̉ndm Аниргүй шөнө Canten Al Rey
Song not available - connect to internet to try again?