1) Yesu yana bakin ƙofa, Yana ta da murya, Ku ƴan Adam duk, ku ji ni, Shiga ƙofar hanyata. 2) Ƙofan nan da wuyar shiga Hanya kuwa ƙunƙunta ce, Masu shiga babu yawa, Sai mutane kima ne. 3) Dukan masu son adalci, Dukan masu ƃacin rai, Masu ladabi a ruhu, Su ke shiga, su kaɗai. 4) Ba da dukiya za mu je ba, Ba kuwa da aniya ba, Ba don aikin nagarta ba, Sai da bangaskiya kaɗai. 5) Wata ƙofa tana nan kuwa, Masu shiga sun yi yawa, Hanyan nan kuwa ke da fādi Za ta kai su halaka. 6) Hanyan nan da sauƙi ta ke, Gama babu kokawa Da jaraba ko mugunta, Ba kuwa masu hanawa. 7) Ba su ganin inda za su, Ba tsammanin halaka. Duniya duk da ruɗin Shaiɗan Su kan rufe idonsu. 8) Tashi, masu laifi duka, Sai ku nemi gafara, Sai ku karƃi kyautar Allah Sai ku riƙa yin godiya.సర్వ సృష్ఠలోని జీవరాశి యంత 耶和华没有忘记你 Měníš hroby v zahrady Mahabbatyńnyń bir ushqyny meniń, jan-dúnıeme tıdi БОЖЕ, КАК ИСКАМ غيرت حياتي ạlrb fy̱ ʿlạh బలమైన దేవుడవు เมื่อลูกวางใจพระองค์ (เมื่อลูกเข้าในพระองค์) Reaching For You Аф-аф ит үреді
Song not available - connect to internet to try again?