1) Yesu yana so ya zauna Cikin zuciyar mutane. Shi ya ɗauke laifofinka Ranka kuma ya ke so. KORUS Yesu yana bakin ƙofa, Sai ka ji maganarsa, Buɗe ƙofar zuciyarka Yi wa Yesu maraba. 2) Akwai dama domin wasa Akwai damar aiki kuwa. Babu wuri domin Yesu Cikin zuciyar mutane. Korus 3) Yau ne lokacin alheri, Akwai ceto dominmu. Kila gobe babu dama, Gobe fa ba tamu ba. Korus 4) Kwanakinmu kamar iska Suna wucewa da sauri. Sai ka tuba, karƃi Yesu Kamin ranar fushinsa. KorusKutsal Kıl Vieni o fonte benedetta جاساما كۇنا ەي حالقىم Dietky srdca nevinného do kostola prišli sme L'amore parlerebbe slạm yswd ḥyạty Несите свет Тебе зове, тебе зове Face to face/ Vision لولا الصليب من انا
Song not available - connect to internet to try again?