YUNANA 1) Ubangiji ya yi magana da Yunana Ya ce "Yunana ka tashi ka je Nineva Ka shaida masu bishara domin su tuba Gama muguntarsu ta hau zuwa gareni." KORUS Mu masu bi yau, mu yi biyayya Ga magana Ubangiji Ubangiji fa ba mutum ba ne Don haka mu yi biyayya da maganarsa. 2)Amma Yunana ya tashi domin ya gudu Daga fuskar Ubangiji zuwa can Tarshish Ya gangara zuwa Yafa ya shiga jirgi Yana murna wai ya gudu a fuskar Allah. Korus 3)Yunana ya manta Allah yana ganinsa Sai Allah ya nuna Ikonsa ga Yunana Ya aiko babban iska da haɗari Sai Yunana ya tuna Allah yana ganinsa. Korus 4)Allah ya shirya babban kifi cikin teku Kifi ya haɗiye Yunana har kwana uku Nan da nan Yunana ya tuna akwai Allah Wane ne zai gudu daga fuskar Ubangiji. Korus 5)Cikin duniya yau akwai irin Yunana Waɗanda ba su so su bi Ubangiji ba Suna ruɗin kansu cewa za su guje shi Suna manta Allah ne mahalicin duniya. KorusGyőzelemről énekeljen Tong Chogʻida ھەمدۇساڭا Туро ситоиш кунам Soha ne félj ДУШАТА МИ ВИКА КЪМ ТЕБЕ kẖrwf ạlfṣḥ ạ̉nạ hjylk bḍʿfy Ry Raiko feno antra ليس بالخبز
Song not available - connect to internet to try again?