1) Zamanin dā, Almasihu Ɗan Allah Ya ji tausayinmu, mu ƃatattu. Shi ma ya rabu da gidan Ubansa Ya shigo duniyan nan tare da mu. KORUS Zuwan Mai Ceto ƙauna ta sa shi, Allah ya bayar don duniya duk, Kada su ƃata, sai dai su sami Ceto da rai kuwa na har abada. 2) Zaman Mai Ceto a wurin mutane Da yawan so da alheri ya ke. Kowa ya nema ya gamu da Yesu. Ya dai same shi mai taimako ne. Korus 3) Zaman nan nasa na aikin alheri, Ba shi da aibi, mai ƙauna ne shi. Ransa ya bayar don fansar mutane, Allah ya karƃa, mai tsarki ne shi. Korus 4) Domin zunubinmu Yesu ya mutu, Bayan ya mutu ma sai binnewa. Shi ma ya tashi a rana ta uku Kāna ya hau Sama wurin Uba. Korus 5) Yesu Mai Cetonmu zai sake zuwa, Haka alkawari wanda ya yi. Sa zuciyarmu dai kowace rana, Bari ya iske mun shirya sosai. KorusЕлате, брате, ела! yʿẓm nṣrnạ О Иисус достоин Ты الناس بيلومونا Z szybkością wiatru كەل، قۇدايعا تاعزىم ەتۋگە Ty v nás Chceme chváliť Tvorcu všetkého تاازئم قىلابىز ىيسا الدىڭدا Јени илдə бир даһа севинҹимиз
Song not available - connect to internet to try again?