1) Zamanin da, Almasihu ya zo Duniya, cetonmu ne ya ke so. Kada mu kasa, mu dai, sai mu kai, Tare mu zauna da ainihin rai. KORUS Wa'azin Yesu, shi mu ke yi, Shi mu ke yi, tsaya ka ji. Kada ka raina, kada ka ƙi, Riƙe da kyau, ka bi. 2) Iko ya karƃa a wurin Uba Domin ya taimake mu, shi ya sa Masu shan wuya da karkatattu Suka zo gunsa, ya hutad da su. Korus 3) Wa'adin Allah ya cika sarai, Nasa Ɗan Rago ya mutu sosai. Aibunsa babu, duk laifinmu ne, Ɗaukar zunubinmu mutuwa ce. Korus 4) Kwanansa uku a binne ya ke, Sai aka gan shi rayayye ne kuwa. Duba, ka ga Ubangiji ne shi, Sanadin ceto ne, shi za ka bi. Korus 5) Ina godiya ga Allah Mai Rai Domin ƙaunarsa a cikin Yesu. Ya ba da Ɗansa don zunubaina, Ya ba ni rai na har abada fa. Korusشهداء وقديسين Canto a te Se tu vuoi yạ mḥbạaⁿ Танринин Гузусу พระประทานหนทาง zhǔ yé hé huá a qiú nǐ shè miǎn E vivo con te Сӧмын Кристослӧн вир пыр Qoldaǵy saýsaqtyń bári on shaqty
Song not available - connect to internet to try again?