1) Ƴan duniya ba sa yarda da Ubangijinmu, A ransu ba sa ɗauka ya zama sarkinsu, Amma fa wata rana zai komo duniyan nan, Gama mulkin duniya duka nasa ne. KORUS Za ya komo wata rana, i, wataƙila yau, Za ya komo daga Sama domin ya fyauce mu, Jama'arsa sai murna tare da shi su ke, Gama mulkin duniya duka nasa ne. 2) Mu, ranan nan sai daɗi mai yawa za mu ji; Ba sauran ƃacin zuciya, ba sauran zunubi, Sai murnar ganin Yesu, Yesu mai fansarmu, Domin mulkin duniya duka nasa ne. Korus 3) Ko yau ne ya ke zuwa, mu ba mu sani ba. Ya ce mu yi ta tsaro, mu riƙa jiransa. Mun sani yana zuwa, ba shakka ko kaɗan. Gama mulkin duniya duka nasa ne. KorusQұdіrettі Qұdaydıń ıdısı bolǵım keledі На земле я имею дом Já dal jsem život svůj قۇداي ٴبىزدىڭ پانامىز Takhta Mulia di Tempat Baka Popolo mio Per la via della vita You are Holy بأمر وبسلطان Behold What Manner of Love the Father
Song not available - connect to internet to try again?