1) A cikin zuciyata na ji muryar Mai Cetona. "Ka zo gare ni nan", ta ce, "In ba ka hutawa". Na zo gun Yesu hakanan, da zunubi mai yawa, Ya saukar mini fa da su, ya ba ni warkarwa. 2) Muryar ta kuma ce da ni, "Ga ruwan rai na bayar. Ka zo, ka sunkuya, ka sha, ka daina ƙishirwa." Na zo gun Yesu fa, na sha daga rijiyar rai. Kishi ya ƙare, na natsu, raina ya wartsake. 3) Muryar Mai Cetona ta ce, "Ni hasken duniya ne. Wanda ya zo gun haskena, ransa zai tsarkake." Na zo na shiga haskensa, ya rayad da ruhuna, Har abada kuwa nan na ke gun Yesu, Sarkina.Ó, Ježiš je Pán Tu sei il mio Dio ยุคสุดท้าย Te alabaran oh Jehova Todos los Reyes Ho bisogno di Te / Uno Нас возлюбя послал Бог Сына ṭbʿk mnạn ᠢᠰᠦᠢᠰ ᠪᠦᠭᠦᠳᠡ ᠶᠢ ᠲᠥᠯᠦᠭᠰᠡᠨ Рассвет يفتح وليس من يغلق
Song not available - connect to internet to try again?