1) Cikin Yesu Almasihu zan dogara. Aikin ceto duk ya cika, zan dogara, Ba a cikin aiki nawa, Ko a cikin nagartata, Sai dai cikin aikin Yesu zan dogara. 2) Cikin giciyen Almasihu, ga gafara. Ko mutane ba sa yarda, ga gafara. Fansarmu wurinsa ta ke, Almasihu Mai Cetonmu, Giciyen ya kai mu gunsa, ga gafara. 3) Jinin Ubangiji Yesu ya wanke ni. Jininsa mai daraja ne, ya wanke ni. Laifina mai dauɗa baki, Jininsa ya tsarkake ni. Cikin jininka, ya Yesu, ka wanke ni. 4) Cikin ƙaunar Almasihu, ga hutawa. Ta fi ƙaunar iyayenmu, ga hutawa. Ƙaunarsa fa ba kamarta. Ko zunubi, ko jaraba, Yesu ne zai ci nasara, ga hutawa. 5) Zuwan Yesu Almasihu na gaskata. Bisa ga alkawarinsa, shi ne zai dawo. Zo da sauri, Ubangiji, Sake halina da jiki, Taka ce sarautar kome har abada.fy ʿyd mylạdk أنت هو صخرة خلاصي Car tu es grand Da-ne putere, Doamne astăzi cerem A fény gyermekei Poď k Bohu v každej potrebe يمكن يوم Sen Hayot Nafasim إبدأ معايا Kamkoľvek pôjdem
Song not available - connect to internet to try again?