1) Da tunawar ƙaunar Mai Ceto. Al'ajabi na ke yi. Ga Yesu ya sha wulakanci Don laifin da ni na yi. KORUS Al'ajabi! Al'ajabi! Wannan waƙa sai in yi. Al'ajabi! Al'ajabi! Mutuwarsa ta cece ni. 2) Dalilin jiƃinsa mai jini Da zafin addu'arsa Ba domin kansa ya yi ba, Sai domin zunubina. Korus 3) Mala'ika ya ji tausayinsa, Ya zo daga Sama can Domin ya ƙarfafa ransa A cikin wahalan nan. Korus 4) Ya ɗauke zunubai duka, Ya maishe su nasa ne. Ya kai su can bayan birni, Dominsu ya ba da rai. Korus 5) A can cikin daraja tasa Zan duba Mai Cetona. Zan rera waƙa gare shi Domin yawan ƙaunarsa. KorusMnie do Nieba dążyć trzeba Grand Dieu, nous te bénissons Ellerimi kaldırdım Gökdäki Atamyz Laisse-moi désormais Príď, Pane milý, príď mi do srdiečka Мой Господь всегда со мною dq bạb ạlqlb ywmạaⁿ Свет Твоего лица ساعدني
Song not available - connect to internet to try again?