1) Duba taron nan mai girma Wanda ba mai ƙirgawa, Suna tsaye gaban Allah, Suna yabon sunansa. Suna rera sabuwar waƙa, Suna ta da murya, Mulki, iko, girma, yabo, Naka ne har abada. 2) Su waɗanda suka fito Daga cikin tsanani, Suka wanke tufafinsu Cikin jinin Almasihu, Suka jure, babu tsoro, Suka raina mutuwa, Sun ci nasara kan Shaiɗan Cikin ƙarfin Ahmasihu. 3) Domin wannan, gaban Allah, Yafaffu da cetonsa, Suna yi masa sujada Kullum, ba mai fasawa. Yunwa, ba sa jinta kuma, Yesu yana kiwonsu, Shi ya shafe hawayensu Daga dukan idanu. 4) Almasihu, muna roƙo, Ubangijin tsarkaka, Taimake mu cikin duniya Mu bi sawun shaidunka. Haka za mu ratsa mutuwa, Za mu shiga mulkinka, Inda Masu Binka duka Su ke yabon ƙaunarka.Господь огонь с небес священный Santo Re Та бол Альфа Омега Nu descuraja pe cale Víc lásky, víc moci Осмонга сен назар сол Oh qué amigo nos es Cristo Venez à Celui qui pardonne أنا عايزك إنت You are my healer
Song not available - connect to internet to try again?