1) Ga alkawari na Allah cikin Littafi Mai Tsarki Yesu ya yi mani shi In kun roƙi kome ne. A cikin sunana dai-dai Shi zai ji addu'arka. KORUS Yesu yana jiranmu mu zo gareshi Kome ya ke damunka Tashi dai ka yi addu'a Wanda ya zo gunsa, za a taimake shi, Lalle yana jin addu'a. 2) Dukan inda biyu ko uku suna nan a tattare Nan ya ke a tsakiya Dukan wanda ya yi roƙo tare da bangiskiya Za a ji addu'arsa. Korus 3) In na kiyaye mugunta a cikin zuciyata Allah ba zai ji ni ba, Addu'ar mai ƙin shari'a abin ƙyama ne ya ce, Allah ba zai ji ta ba. Korus 4) Bari dai mu yi addu'a kullum ba da fasawa Domin duka tsarkaka, Mu yi tsaro fa a ciki, mu yi tare da godiya Allah yana jin addu'a. KorusYücelik, bilgelik Senindir Rab Come and praise him royal priesthood Սիրտս Քոնն է Տեր ربي إني أحمدك Take courage Сьозлерин Биттии Йер ạ̹dy lh frṣẗ Abbiam bisogno di te О ЧУДНА МИЛОСТ БОЖИЯ Ó, Ježiš je Pán, On korunu vzal
Song not available - connect to internet to try again?