1) Ga Allah kaɗai, Mahiliccinmu, Daidai mu yi waƙar yabonsa yanzu. KORUS Mu yi waƙar yabon Allah Addu'ar za mu yi. Mu yi waƙar yabon Allah, Mu girmama shi. 2) Mu girmama shi, addu'ar za mu yi. Mai kyauta ba gori duk baiwa sai shi. Korus 3) Mai raya mutum kyautar, Allah sosai Ban da Allah, ina za mu sami jinƙai? Korus 4) Jinƙai ne ya sa ya yi mana baiwa Da ya aiko Mai Ceto tun zamani dā. Korus 5) Mai Ceto ne shi wanda Allah ya ce Shi Ɗansa ne, ransa ya so shi sarai. Korus 6) Labarin Mai Ceto da daɗi ya ke Mutuwassa da tashinsa duk namu ne. Korus 7) Duk wanda ya ce Almasihu zai bi, Tsattsarken numfashi zai ƙarfafa shi. KorusDari IV Track 10 ạlḥrb ạlrwḥyẗ - jzʾ tẖạn كل يوم تحت صليبك كنت بافكر yạ sydy ạ̉nt ạlḥbyb Radostná novina ربي يسوع لي Бүкіл әлем Құдайдың қолында Sionon a kürt zengjen Chvála Ti Kriste Odpustené moje viny
Song not available - connect to internet to try again?