1) Ga mutum mai ƙazamin Ruhu Ya gamu da Yesu dai Kullum kuwa ko dare da rana Yana kururuwa dai. Ya tsatsage jikinsa kuwa Can kabari da duwatsu. 2) Ba wanda na da iko shi damre Mai ƙazamin Ruhun nan Sau da yawa ya tsutsunke Har sarƙoƙi ya karye su. 3) Sai ya iske Yesu na zuwa Daga nesa ya iske shi Ya sheƙo a guje domin Ya yi masa sujada fa. 4) Ya ce "ina ruwana da kai, Yesu kai Ɗan Allah ne ?" Ya ce "Ka fito daga cikin Mai ƙazamin Ruhun nan." 5) Ҡazamin ruhohin nan Sun shiga cikin gursunnai Su sun faɗi cikin teku Sun nutse dai, sun shaƙe kuwa. 6) Ta wurin ikon Maɗaukaki Yesu Ɗan Allah kaɗai Mai ƙazamin ruhun ya zama Mai hankali, mai shaida kuwa. 7) Sai mu bi Yesu don ya iya Cece mu daga Shaiɗan. Mu gaskanta shi Ɗan Allah ne Mai Cetonmu, Mai Kamnarmu.Signor Gesù io amo te عايشين معاك في هنا Исо Подшоҳ Emeld fel a kezed Haleluja, spasenie, sláva i moc Beytlehem mạ ạ̉ḥly̱ ạlsjwd mʿny̱ ạlḥb Salvatorul bun te cheamă Słyszę ja mię wzywa Jezus
Song not available - connect to internet to try again?