1) Ga taro can mai girma kuwa, har ba mai ƙirgawa, Al'ummai, dangi, harshe duk, kowane iri kuwa, Suna tsaye gun Allahnsu, yafe da adalci, Ga shaida kuwa ta nasara a cikin hannunsu. 2) Sun ta da murya kuwa sun ce, ceto ga Allahnmu, Yabo ya hau ga Allahnmu, duk da Mai Cetonmu. Mala'iku da dattawa sun haɗa bakinsu, Sun fāɗi bisa fuskarsu loton sujadarsu. 3) Albarka, girma, godiya, ga Allah, suka ce, Wadata, iko, ceto kuwa, har dukan zamanai. Yafaffun nan, ka shaida su? Daga ina su ke? Rigunan nan da suka sa, don me walƙiyarsu? 4) Domin maganar shaidarsu, tun suna duniya, An kashe su don suka ƙi su yi musun Yesu. I, domin shaida ga su nan, ba shakka, ba tsoro. Hidimar Allah za su yi dare. da rana kuwa. 5) Yunwa ba za su ƙara ji ko ƙishi ba daɗai. Rana ba za ta buga su a gidan Allah ba. Ɗan Allah ne mai kiwonsu, shi fa zai bi da su. Hawaye daga idanu, Allah zai share su.متكلي أنت إلقاء 1 Cross Dünyanın sonu geliyor Yesus Kawan yang Sejati tʿbt fqlt ạ̉jyb ndạh Hәsr Edirәm Hәyatımı 中国人要起来 Laat Die Hele Aarde juig ạ̉nt mlk ạlmjd
Song not available - connect to internet to try again?