1) Ga Yesu Ubangijinmu. Mai Ceton duniya. Mutane, kome yawansu, Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa. 2) Ku manya manya, Allah ne Ya ba ku daraja. Babbanku, Yesu, yana nan, Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa. 3) Ku yara duk, ku neme shi Tun yana samuwa. Da ƙarfi da ƙuruciya Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa. 4) Ku mata, ƙaƙa za ku yi? Ku girmama Yesu. Mai Ceto Almasihu ne, Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa. 5) Ku masu rashin ganewa, Ku masu lalube, Mai korar duhu, ga shi nan. Ku duk, ku riƙa zuwa yabon girmansa. 6) Ga Yesu Ubangijinmu, Mai Ceton duniya, Mutane, kome yawansu, Su duk, su riƙa zuwa yabon girmansa.Xudovandni madh etinglar Таится враг на жизненном пути nfsy trjʿ Lord of Hosts Cieszę się wciąż Vec predivná, neslýchaná Sevinin, benim yavrular НЕ Е ЛИ ТОЙ In ogni momento Noc v Getsemanskej záhrade
Song not available - connect to internet to try again?