1) Ina yabon sunan Yesu, shi ne Mai Cetona, Cikin duniya duka babu kininsa. Zunubaina masu yawa ya yafe mini duk, Har ya tsarkake ni cikin jininsa. Wahala ko ta zo ne, ko daɗi na ke ji, Sai in sani yana nan tare da ni. Yesu ne ya ba ni iko, Shi ne mai nasara, Ba zan rabu ba da shi har abada. 2) Shaiɗan ya kan jarabce ni, amma idan na je Wurin Yesu, ya kan ba ni nasara. In na karanta Littafi, in yi addu'a kuwa, Za ya ji ni har ya ba ni taimako. Ko duniya duk ta ƙi ni, ba zan ji tsoro ba, Sai in ci gaba a cikin hanyar rai. 3) Ba zai bar ni ba a duniya in zauna, ni kaɗai, Za ya kiyaye ni cikin ƙaunarsa. Sai in yi masa biyayya, in aika nufinsa, Ina dogara ga ikon Ruhunsa. Ya shaida za ya dawo ya kai ni gidansa, Inda zan ga fuskarsa har abada.Sonsuza Dek Кто сотворил весь мир Nous venons dans ta présence Вот моя жизнь пред Тобой Бог Nuovi cieli e nuova terra Cerco di trovare le parole Как тяжело любить Görkem Kralı Ce folos de viaţa ta pribeagă lạ̉nh yswʿ
Song not available - connect to internet to try again?