1) Jinin Yesu mai daraja yana zubowa Domin fansar duk jama'a, domina. KORUS Jinin Yesu mai daraja za ya tsarkake Wanda za ya zo ya karƃa, kyauta ce. 2) Ko da zunubanku sun yi kamar mulufi, Cikin jinin Almasihu za su fita. Korus 3) Ba abin da za mu biya, duk ya ƙarasa Yesu yana miƙa mana gafara. Korus 4) Cikin wuri mafi tsarki sai mu shiga fa, Don ta wurin jinin Yesu mun tsarkaka. Korus 5) Kome kokawa da Shaiɗan, akwai nasara. Gama cikin jinin Yesu iko 'na nan. Korus 6) Ran da za mu shiga Sama, sai da jinin nan, Za mu yabi sunan Yesu ranan nan. Korusيسوع زي السكر Pane, prijmi ma ạrtfʿ ʿly̱ ạlsmạwạt Rab Lütfun Yeter Det var nåde 涛声依旧 Znam drzewko najśliczniejsze Кусурсуз Курбан لأنة تعلق بي - موسيقي Hayranlıkla Severim Seni
Song not available - connect to internet to try again?