1) Ku ta da zuciyarku, kada ta ƃaci kuwa, Ƴanuwan ba su mutu ba, su barci su ke yi. An shirya zamansu a gidan Sama can, Allahnmu ne ya kira su su fita duniyan nan. 2) Ba sauran zunubi, jaraba ba ta can, Wahala duk da ƃacin rai ba za su shiga ba. Su, Yesu su ke bi da muryar nasara, Sunansa yana goshinsu, sun duba fuskarsa. 3) Mun ajiye jikinsu can cikin kabari Har ran da za a ta da su marasa ruƃewa. Shi Yesu Fansarmu, shi ne mai ba da rai, A cikin rashin ruƃa dai, shi za ya ta da su. 4) Mun gode, Allahnmu, domin bangaskiyarsu, Don shaidarsu a wurinmu, kwatancin halinka. Ya Ubangijinmu, ka ƙarfafa mu yau Domin mu bi sawunsu har mu gama aikinmu.ربي يسوع بأحبك Только Ты победил Эслагин Мени Сенің Киелі Жүзіңнен قومى أستنيرى Кенелт Рухыңа Underfullt Jesus elsket ạrḥmny yạ ạllh 送给你在主里的父母 You Are Worthy
Song not available - connect to internet to try again?