1)Ku yi ta wa'azi wurin mutane duk, Gama a duniya akwai wahalar rai. Bari duk Masu Bi su shaida ko'ina, Mai Taimako ya zo. KORUS Mai Taimako ya zo, Mai Taimako ya zo, Ruhu Mai Tsarki da Allah ya aiko. Ku labartad da shi wurin mutane duk, Mai Taimako ya zo. 2) Mun sami haskensa, ya watsa duhunmu, Ya kau da tsoro duk, ya ba mu kwanciyar rai. Ya kawo gafara ta dukan zunubi, Mai Taimako ya zo. Korus 3) Ga Ubangijinmu, ya zo da warkarwa. Ga ƴaƴan duniya, ruɗaɗɗu na Shaiɗan. Ya kwance ɗaurarru, ya kawo fansarsu, Mai Taimako ya zo. Korus 4) Ya Allah mai ƙauna, ko ni na iya ƙi In shaida j inƙanka ga dukan mutane? Ga ni da, matacce, ka ba ni sabon rai, Mai Taimako ya zo. Korusshān gǔ zhōng yǒu yī duǒ kū qì de bǎi hé huā Living With A Fire تأمل 2 Ty, Bože náš (acoustic) Han er alt for meg Ветви дорог Hosanna Synowi Dawidowemu Kuřátka spí أنت الرب ملك 让小孩子快来
Song not available - connect to internet to try again?