1) Mai Ceto yana ƙaunata, Shi Makiyayina ne. Tun Yesu yana kiwona, Ni ba na rasa kome. KORUS "Ku zo gare ni, dukanku, Ku masu nauyin kaya, Ni ma in ba ku hutawa," In ji shi, Masoyina. 2) Dā ina zaman tayarwa, Na ƙi tafarkin Yesu, Sai ƙaunarsa ta jawa ni, Ta sa ni cikin garke. Korus 3) Nan gaba dai, Ubangiji Kullum zai bi da raina A cikin hanyar adalci Sabili da sunansa. Korus 4) Ko cikin kwarin mutuwa, Ba zan ji tsoro ba fa, Ba wanda za ya taƃa ni, Tun Yesu yana sona. Korus 5) Ƙaunarsa marar ƙarewa Nan gaba za ta bi ni. A cikin gidan Allah kuwa Har abada zan zauna. KorusTANRININ SEVGİSİ Amore fù xìng de shí kè yǐ jīng lái dào Psalm 150 Zrak viery upieram Mai più schiavo Gör Gör Gör Ты Царь Ты Бог неба и земли Сени араян херкес qdmwạ llrb yạ ạbnạʾ
Song not available - connect to internet to try again?