1) Mai kiwona shi Yesu ne, Duk tsoro dai ya kawu. Ni ba zan rasa kome ba, Ga kulawa mai kyau fa! 2) Abinci dai a yalwace, Ga ruwan sha domina. Ban rasa kome ba domin Yesu ne makiyayi. 3) Har raina ma ya wartsake. Yanzu dai Yesu ya sa Shawararsa ta bi da ni A duk tafiyata ma. 4) Har cikin kwarin mutuwa, In dai ya sa in je can, Tafiya tare mu ke yi, Zai tsare ni sosai kuwa. 5) A idon su maƙiyana Abinci ma ya shirya. Da mai ya shafe kaina har Sai daɗi na ke ta ji. 6) Alheri duk da jinƙansa Yesu ya sa su bi ni. Don haka daɗi na ke ji Kullum a wannan duniya. 7) Mai kiwona shi Yesu ne, Ba fashi, ko kaɗari ma, Har gidansa madauwarni, Mu je mu zauna tare.تأمل 4 ạ̉nạ ʿạyz ạkwn dạymạaⁿ fy̱ ḥḍwrk Hosanna pour le Roi! Duchu Święty przyjdź Ты поймешь меня Dziękuj Mu 찬양과 존귀 주께 Szeretlek, Jézus О Божья мощная рука كيف أنسي سيدي الغالى
Song not available - connect to internet to try again?