1) Mu yabi Yesu tare da mala'iku (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 2) Mu tada murya tare da mala'iku (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 3) Mu ɗaukaka shi, mu ba shi girma (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 4) Mulki da ikon sarauta nasa ne. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 5) Mu ce "Mai Tsarki" tare da mala'iku. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 6) Shi ne tushin Dawuda, ya ci nasara. Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 7) Mai isa ne kai fa ka ɗauki littafin. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 8) Ka buɗe littafin da hatimansa bakwai (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 9) Ka karanta duka asirin Allah. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 10) Kai ne Allah tun fil azal ma. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 11) Mun gode, ya Allah, don ɗanka Yesu. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 12) Ka sayi mu da jini naka. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 13) Mu raira waƙa tare da mala'iku. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku. 14) Mu pansassu ne na Yesu Kristi. (2x) Halleluya, halleluya, in ji mala'iku.hl ystṭyʿ ạlrb by Pan mnie strzeże mlk ạlmlwk wjlạlk Nu pierde vremea degeaba ВГЛЕЖДАМ СЕ ВЪВ ТВОЯТА СВЯТОСТ Гьоркемли Раб'бим Singurul motiv de laudă Всё могу в Укрепляющем меня Дали сал кроткият Исус Žalm 34
Song not available - connect to internet to try again?