1) Mu yi sujada ga Ubangiji, Mu yi godiya domin ƙaunarsa. Da zuciya ɗaya mu ɗaukaka shi, Mu yabi sunansa da duk ladabi. 2) Mu yi tunani a kan girmansa, Mu yi waƙoƙi kan alherinsa, Mai Tsarki, Mai Ƙauna, Mai Gaskiya ne, Mai ikon halitta, mai jin addu'a. 3) Bukatarmu duk shi ya ke ta biya, Mu karƃe su fa tare da godiya. Abinci, abin sha, numfashi da rai, Lissafin kyautansa ya fi ƙarfinmu. 4) Mu raunana ne, amma cetattu, Mu ƴaƴansa ne, bai yashe mu ba. Yana marmari dai mu yi zumunta, Jiƙansa mai yawa, ba misalinsa. 5) Al'amuranmu su girmama shi, Da bakunanmu mu yi ta shaida. Mu bauta masa, mu ji tsoronsa kuwa, Gama shi ne Allah na duk duniya.愿神兴起时代的工人 Jésus, mon Sauveur, pourquoi Seigneur, tu es ma référence เพราะพระเจ้าเป็นความรัก Langit Dan Bumi Cerah Dan Terang На ладонях счастье держит мой Христос واحدة سألت Зачем так мучаешь себя Tak Bóg umiłował Я так устал
Song not available - connect to internet to try again?