1) Muna son wurin nan na darajar Allah. Murna ta ɗakin na ta fi a kwatanta. 2) Ɗakin addu'a ne na taron bayinka. Lalle fa kana nan tare da jama'a. 3) Wurin Baftisma fa mu ke sonsa ƙwarai, Gama nan Ruhunka ke ba da alherai. 4) Muna son Tebur ma, wuri ƙaunatacce. Nan ka ke ciyad da mu cikin bangaskiya. 5) Maganarka ta rai, ita ma mu ke so. Ta ba da kwanciyar rai, salama ta kan kawo. 6) Yanzu mu ke ta yin waƙa ta jinƙanka, Amma can Sama fa da waƙar nasara. 7) Ya Yesu, ƙara dai alheri da ƙauna Ga mu jama'arka, mu dinga sujada.Lord, keep us safe this night / Combe Martin Аз чакам 耶稣永爱我 Алла сулары سنرنم ونهلل Uzbekiston yurtida tugilanman Sonsuzca Kutsal بركات الرب Сен Йюджесин Раб Yo mucho me alegré
Song not available - connect to internet to try again?