1) Ran da aikinmu ya ƙare cikin wannan duniya, Za mu hau mu zauna gun Mai Cetonmu, Za mu huta daga ƙuncinmu, mu yi ta zamanmu Wurin Yesu Kristi, Ubangijinmu. KORUS Za ya kira mu a Sama, Za mu shiga gaban Allah, Za mu wurin Mai Cetonmu, Zuwa gidan da ya shirya dominmu. 2) Can a gida mai darajan nan, a gaban Allahnmu, Za mu yi sujada gaban kursiyinsa, Za mu haƙa kai da Masu Bi na dukan zamanai, Za mu yi ta yabon Yesu, Mai Ceto. Korus 3) Can mā gane duk dalilin ƙuncinmu a duniya, Za mu gane yawan ceton da ya yi. Za mu yi ta yin godiya domin dukan aikinsa, Za mu yabi sunan Yesu, Mai Ceto. KorusЖүрегіммен Ouvrez les portes du saint lieu Ni en la tierra ni en el cielo Deyil güzel sözler ile ạ̉yhạ ạlạ̹nsạn El Shaddai Быть лицом к лицу с Иисусом Пред Иисуса именем Regnerai per sempre GADOL ADONAI
Song not available - connect to internet to try again?