1) Ran da aikinmu ya ƙare cikin wannan duniya, Za mu hau mu zauna gun Mai Cetonmu, Za mu huta daga ƙuncinmu, mu yi ta zamanmu Wurin Yesu Kristi, Ubangijinmu. KORUS Za ya kira mu a Sama, Za mu shiga gaban Allah, Za mu wurin Mai Cetonmu, Zuwa gidan da ya shirya dominmu. 2) Can a gida mai darajan nan, a gaban Allahnmu, Za mu yi sujada gaban kursiyinsa, Za mu haƙa kai da Masu Bi na dukan zamanai, Za mu yi ta yabon Yesu, Mai Ceto. Korus 3) Can mā gane duk dalilin ƙuncinmu a duniya, Za mu gane yawan ceton da ya yi. Za mu yi ta yin godiya domin dukan aikinsa, Za mu yabi sunan Yesu, Mai Ceto. KorusЯ верю Господь в Твоё воскресенье Oro e argento Hari Ini Tuhan Berkati Srdce mého Král zuó rì de zhōng xīn diū zài nǎ ér Гел Ей Джанъм mạ ạ̉ḥly̱ ạlsjwd زيك أنت dmʿẗ wạ̉nẗ JESUH NIH AN KHAMH CANG
Song not available - connect to internet to try again?