A Kabari kan giciye,
Na ga ƙaunar Ubangijina,
Na ba shi dukan zuciyata.
Wahalata shi ne ya sha,
Wane ni fa har da zan ƙi
In karƃi kyautar cetonsa?
Ga raɗaɗinsa domina.
Ya Ubangiji, karƃe ni,
Ka yafe mini laifina.
Don dukan aikin cetona,
Na ba ka rai da zuciya duk,
Ni naka ne har abada.