1) Su magauta dayawa ne a kewaye da mu. Shaiɗan da dukan runduna sun zo su kā da mu, Amma an shirya makamai don wannan yaƙi fa. A cikin sunan Yesu ne za mu ci nasara. KORUS Yesu mai nasara, Yesu mai nasara, Da sunan Yesu ne mu ke yin nasara. 2) Kwalkwalin ceto bisa kai, ɗamarar gaskiya, Da garkuwa ta bangaskiya, sulken adalci ma, Shirin bishara takalmanmu ne a ƙafafu, Ga takobi na Ruhu ma, wato Maganarsa. Korus 3) Mu yi addu'a koyaushe, mu yi aniya fa, Mu yi roƙo da naciya don dukan tsarkaka, Mu tsaya dai da ƙarfi fa, mu yi tsayayya ma, A cikin ikon Yesu ne za mu ci nasara. KorusPodnieśmy głosy, śpiewajmy Владыка Utíchla už vrava sveta, zhasol slnka jas Asma ve Dalları Credo in te ạ̉nạ wạtẖq Таков как есмь без дел без слов lmạ bkyt mn jrḥ fy qlby Len tebe patrí sláva О, Құдай қарашы маған
Song not available - connect to internet to try again?