1) Suna nan, su tumaki tasa'in Da tara lissafinsu, Amma ɗaya ta bace a garken nan, Ta yi nisa da sauransu. Ita kaɗai, ga dare ya zo, Can a jeji, ba taimako, Can a jeji, ba taimako. 2) Ga waɗannan duka sun kwanta nan. Ko su ba su isa ba? Mai garke ya amsa, ko kaɗan, Zan je neman ɗaya ɗin nan. Can ya tafi da azabar rai, Can ya iske ta, abin tausayi, Can ya iske ta, abin tausayi. 3) Amma zafin wahalar da shi ya sha Ba wanda ya taɓa ji. Har ya sami abinsa da kyar da rai, Da jinƙai ya ɗauke ta. Da ɗari da ciwo ya iske ta can A bakin mutuwa, tinkiyan nan, A bakin mutuwa, tinkiyan nan. 4) Ga jini a hanya a sarari, Ya bi sawun makiyayi. Ai, ya zubar da shi garin hanzari, Domin zafin ƙaunarsa. Ƙaya ta soke shi, jeji ya bi, Dutse ya buga, ba ganin gari. Dutse ya buga, ba ganin gari. 5) Alhamdu ga Allah mai runduna, Alhamdu ga Almasihu. Mala'iku na Sama sun ɗaukaka shi Mu ma, muna yin godiya. Muna yabonsa, ya cece mu, Mu, muka ƃace, ya komo da mu, Mu, muka ƃace, ya komo da mu.Allah'ı Kim Ararsa قصاقيص Un solo cuore Una porta aperta ربي تاجي إنت الحياة Ты устала душа в непосильной борьбе Hiç görmedi insan güozü لإلهنا المخلص SMS
Song not available - connect to internet to try again?