1) Ta wurin ƙaunar Mai Ceto, sai lafiya. Ƙauna ba ta sakewa kuwa, sai lafiya. Jininsa mai tamani ne, ƙaunarsa har abada ce, Idonsa ya tsare mu dai, sai lafiya. 2) Ko da muna shan wahala, sai lafiya. Shi ya iya cetonmu duk, sai lafiya. Murnarmu daga Uban ce, ladanmu daga Yesu ne, Tsarkakewarmu ta Ruhu, sai, lafiya. 3) Bege kuwa ya haskaka mu, sai lafiya. Bangaskiya ta ƙarfafa mu, sai lafiya. Mun dogara kuwa ga Allah, Yesu ne ke biyan bukata, Ko a mace ko a raye, sai lafiya.Les cieux proclament Rabbin Sesi فوق كل قوة ورياسة - Above all powers هيا بفرح نشدوا للرب Хвалю Цябе ạ̹nt ạ̉ḥn ʿly Kynçylyklaryň içinde Ubangiji Shi Ne Komena ИМАМ МИР ВЪВ СЪРЦЕТО Bizler Rab'bi Sevmek İçin Yaratıldık
Song not available - connect to internet to try again?