1) Ubangiji, muna gaisuwa, Mun gaishe ka, Sarkinmu, Kai mai shan wahala tamu, Kai mai cika cetonmu, Kai, bayanin ƙaunar Uba, Yesu, Dan Maɗaukaki, Naka suna mu ke kira, Yesu Ubangijinmu. 2) Kai ka kau da zunubanmu, Rauninka dominmu ne, Mutuwarka ta sayi ranmu, Kai ne Mai Cetonmu dai. Can dominmu ka ke roƙo, Kana shirin gidanmu, Kana jiranmu da ƙauna, Yesu Ubangijinmu. 3) Kome girman sunan kowa, Ba zai kai ga naka ba. Kome yawan daɗin duniya Ba ya kai ga daɗinka. Baki ba ya iya faɗi, Kunne ba ya iya ji, Ko misalin naka daɗi, Yesu Ubangijinmu. 4) Tara manyan duniya duka, Duk da yawan girmansu, Har mala'iku na Sama, Ba su kai ka girma ba. Ko har abada bayinka Muna yi ta yabonka, Dukan yabo sai ya kasa, Yesu UbangijinmuMy Glorious 若有人自以为虔诚 LORD DISMISS ME Я не имею то, что есть у всех Kiranya Anug'rah Kristus bʿdmạ kạn Yücedir 我多想飞 إنت خلاصي هللويا أنت نور العالم
Song not available - connect to internet to try again?