1) Ya Allah, miƙa hannunka, ka tsai da haukansu, An kashe Almasihunka ta hannun miyagu. 2) Ba za ka bar Mai Tsarkinka cikin kabari ba. Ba za ka bar maƙiyansa su ci nasara ba. 3) Dā, kayayuwa tsinana sun soki goshinsa. Yanzu ka naɗa Almasihu a hannun damanka. 4) Shi wanda aka kunyata a cikin duniyan nan, Ka tashe shi da daraja, ka ba shi girma can. 5) Shi ne ya mutu dominmu, ya ɗauki giciyensa. Mun sami rai da lafiya ta wurin dūkansa. 6) Idan mun mutu tare nan, mun ɗauki giciyensa, Tare kuwa za mu yi murna a cikin mulkinsa. 7) Ina misalin yabonka, ya Yesu Almasihu? An sanya mulkin kome nan ƙarƙashin sawunka.Santo Spirito (Niente vale di più) Titok és ajándék whạʿysẖ lk Sizni ulugʻlashchun Дякую за хрест Твій Ciągle niezdecydowany أوعى تفكر إني نسيتك mn bʿd snyn wsnyn سمعت صوتك يدعو Ya Rab Sevgin Tükenmez
Song not available - connect to internet to try again?