1) Ya Allah, muka shuka iri a gonarmu, Amma, ya Ubangiji, ka ba da amfani. Ga hatsi, ga dankali, wake da shinkafa. Su muka yi ta noma, sun kuma nuna yau. Kai Mahaliccinmu, ka ba mu kyautarsu, Mu yi godiya, mu yi godiya, domin amfaninsu. 2) A gona mu ke aiki, amma, ya Allahnmu, In ba ka sa albarka ba, ina amfaninsu? Ka ba da hasken rana, da ruwa mai yawa, Kai ne ka shirya ƙasa da daɗin iska kuwa. Kai Mahaliccinmu, ka ba mu kyautarsu, Mu yi godiya, mu yi godiya domin amfaninsu. 3) Amma, ya Ubangiji, dubi zukatanmu, Yanzu ta wurin Ruhunka, maishe su gonarmu. Maganarka ce iri, ka ba mu ikonka Domin ta daɗa girma, ta shaida zamanka. Ya Mahaliccinmu, ka sa albarkarka, Har raina duk ya lura da irin Maganarka. 4) Ni, zan tafi wurinka sa'ad da na rasu, Zan kai amfanin gona, gona ta zuciyata. Ga ƴaƴan raina kuma, ƴaƴan Maganarka, Gare ka duk zan kawo do min albarkarka. Ya Mahaliccinmu, ka sa albarkarka, Har raina duk ya lura da irin Maganarka.Inoyat الله منيح معي Mpivahiny aho eto Благодать и мир Ырайымың, Теңир, бизди Zvončekov zvuk Dengan KasihMu, ya Tuhan Не Мутлу Слышу плач по всей земле Кто без Тебя я Господи
Song not available - connect to internet to try again?