1) Ya ku ƴanuwa, bar bin duniya, Ta da murya domin Yesu. Yafa makamai, dukansu sosai, Shiga Yaƙin Ubangijinmu. KORUS Tashi zuwa yaƙin Almasihu, Tuƃe nauyin kayan duniya, Gaba dai, ba za mu waiwaya ba, Ubangiji Shugabanmu ne. 2) Kome jaraba, muna cin gaba, Lalle za mu ci nasara. Ikon magauci ba mu raina ba, Amma dai ba za mu bi shi ba. Korus 3) Ubangijinmu, ji addu'armu, Ba bayinka dai ikonka. Muna dogara ga Maganarka, Mu da kanmu ba mu iya ba. Korus 4) In mun gama nan, za mu huta can Gidan Allahnmu har abada. Ladan aikinmu yana jiranmu, In mun yi shi da aminci fa. KorusTirik Xudoyimsan Môj milý Ježišu Shox liboz شوقى أن أحيا يسوع Hvor stort i denne siste tid ᠦᠵᠡᠰᠬᠦᠯᠡᠩ ᠲᠡᠢ ạ̹lqạʾ 4 من لي سواك zhǔ wǒ zūn suì nǐ sẖkwn ạ̉nạ yạrby
Song not available - connect to internet to try again?