1) Ya Ubanmu, ka bishe mu Cikin wannan duniya. Kai kaɗai mai taimakonmu, Dube mu da ƙaunarka. Ba abin da za mu rasa, In ka zama jigonmu. 2) Ya Mai Ceto, ka yi jinƙai. Ka san kumamancinmu, Kai ka sha wahalar giciye, Domin fansar dukanmu. Za mu jure har matuƙa In ka sa albarkarka. 3) Sauko nan, ya Ruhun Allah. Cika mu da ikonka. Ba mu ƙauna da salama, Murna marar iyaka. Haka za mu ratsa duniya, Har mu isa gidanka.Pane, zmiluj sa III. Yüreğim Yanlış Yoldaydı Свечи зажжём افرحي أيا نفسي Qutqardyń bar adamzatty kúnádan I går, i dag, til evig tid ربي قد صرت Vicino a Lui Адонай 목마른사슴이
Song not available - connect to internet to try again?