1) Ya Yesu Almasihu, na zo gare ka yau. Da raina duk da ruhu, ka karne su yanzu. Kullum in zama naka, in bi ka, kai kaɗai. Yau nufina na ba ka, duk nawa naka ne. 2) Ya Ubangiji Yesu, kai ne muradina. Ka zo ka gyarta raina, ka ɗauke zunubai. Ya Ruhun Ubangiji, zauna a zuciyata. Ga kasawa gare ni, ka zo da ikonka. 3) Na gode maka, Yesu, ka zama sarkina. Tun daga nan a duniya, ka ba ni nasara. Ko zunubi, ko Shaiɗan, ba sa yin mulkina. Kai ne ka ba ni ceto, i, rai har abada.Å hvor salig å få vandre mmlwỷyn Укрепляется сердце моё Ey şanı yüce Olan Manisnya Nama Penebus تۇر، جارقىرا بئر تۇۇعانىم Lo, He comes with clouds Tsaroanay tokoa izao Gece Gündüz Ağlıyom Figlio mio
Song not available - connect to internet to try again?