1) Ya Yesu, ga ni gabanka, Domin in koyi gaskiyarka. Ka nuna mini cin gaba Da ni zan yi a hanyarka. KORUS Ya Yesu, buɗe idona, Domin in gane hanyarka, Ka nuna mini nufinka, Ya Mai Ceto. 2) Ya Yesu, buɗe kunnena, Domin in ji maganarka. Ni ina so in bi nufinka, In yi abin da ka ke so. KORUS Ya Yesu, buɗe kunnena, Domin in ji maganarka, Ka nuna mini nufinka, Ya Mai Ceto. 3) Ya Yesu, buɗe bakina, Domin in shaida ko'ina Ceton da ka yi wa duniya Da gafarar zunubanmu. KORUS Ya Yesu, buɗe bakina, Domin in shaida cetonka, Ka nuna mini nufinka, Ya Mai Ceto. 4) Yesu, juyad da zuciyata, Domin in nuna halinka Ƴanuwana su dube ni, Har su ga Allah cikina. KORUS Yesu, juyad da zuciyata Domin in nuna halinka, Ka nuna mini nufinka, Ya Mai Ceto. 5) Ya Yesu, ba ni zarafi Domin in yi ta aikinka, Ƴanuwana su rinjayu Su ma su shiga hanyarka. KORUS Ya Yesu, ba ni zarafi Domin in yi ta aikinka, Ka nuna mini nufinka, Ya Mai Ceto.Ааламды жараткан улуу, күчтүү Кудай فن فن فن lyk kl ạlạ̹krạm Tonga ny andro malaza Faites ceci en mémoire de moi 我要服侍主 ạ̹tʿlmy̱ yạnfsy̱ My Koning Heer Mój Boże, w ręku Twym Ojcze mój kocham Cię
Song not available - connect to internet to try again?