1) Ya Yesu, rijiyar kwanciyar rai, Sunanka ta'aziyya ne. Kome wahalar duniya, Kome kuwa fushin magauta, Zuciyata ba ta ƃaci ba, Na ƃuya cikin sunanka. 2) Sunanka gwanin daɗi ne, Faranta zuciya ya ke yi Ko raina duk ya duhunta, Har ya fi dare duhu ma, Duhuna sai shi warwatse, Sunanka tashin rana ne. 3) Kome na rasa, ga shi nan, Maganin kome Yesu ne. Ban damu da talauci ba, Ban mai da tsiya kome ba. Tun da ban rasa Yesu ba, Raina ya kwanta lafiya. 4) Abin da ya same ni duk, Raini ko wulakanci kuwa, Ƙanƙanci, kunya, damuwa, Zalunci, ɗauri, kisa ma, Ba zan ji tsananinsu ba, Yesu zai tsare zuciyata. 5) Gafarar dukan laifina, Ikon rinjayar halina, Sakankancewar ƙaunarka, Salama ba ta duniya ba, An kintsa dukan cetona, Ya Yesu, cikin sunanka.Бир гюн геледжен Мне нужен ты lèi shuǐ yī cì cì mó hú le yǎn jīng Te rog să vii o sfinte Doamne Voia Ta nu voia mea Младенец Иисус Та мэдэх үү? ماسك إيدي İşte Tanrı Benim Yardımcımdır Dari II Track 05
Song not available - connect to internet to try again?