1) Yau ranar murna ce ga mu masu bin Yesu Domin jinkansa, da alherinsa Sai ku zo mu yi tsale, mu ɗaukaka Allah Uba Domin ƙaunarsa, a garemu Domin cetonsa, ta wurin Yesu ɗan Allah Solo: "Sai ku zo." KORUS Sai ku zo mu yi murna Mu ɗaukaka Allah Uba Mu miƙa godiyarmu Ga Allah mai kamnar duniya Solo: "Sai ku zo." 2) An haifi Yesu a Baitalahmi Daga budurwa, Maryamu Aka haife shi, a cikin garke Aka naɗe shi..., cikin tsummoki Shi ke ɗan Allah, mahalicin Sama da kasa Solo: "Sai ku zo." 3) Ruhun Yahweh, yana a kansa Ya rufe shi da rigar adalci Ya aiko shi..., don ya kawo yanci Ga waɗanda, ke cikin zunubi Don Ya bamu rai, na har abada abadin Solo: "Sai ku zo."Senza di Te Peuple chrétien Fissa gli occhi in Gesù 为爱歌唱 เราจะเข้ามาสรรเสริญ hạqdr ạgẖfr اجذبني ضمني إليك Тебе подобным Beytlehem Güzel Bir Sabaha Uyanıyorsun Отец Святой я прихожу к Тебе
Song not available - connect to internet to try again?