1) Yesu Ubangijinmu ne, Mun ƃuya cikin ƙaunarsa. Ba zai kori mai tuba ba, Mu zo mu ba da gaskiya. KORUS I, Yesu ne Mai Ceto, mai ƙaunarmu, Mu karƃe shi, mu karƃe shi. Ya ba da ransa domin laifinmu, Za shi yi mana gafara. 2) Dā, nan a cikin duniya, Mutane suka ƙi binsa, Amma mu dai mu karƃe shi, Mu zama Masu Bin Yesu. Korus 3) Ko muna yi ta aikinsa, Ayyuka ba su cetonmu, Sai dai mu ba da gaskiya Ga mutuwar da ya yi dominmu. Korus 4) Yesu shi ne mai zuwa kuwa, I, za ya komo duniyan nan. Mu yi shiri don zuwansa, Shi kai mu zuwa Sama can KorusЛюблю я fy kl ạ̉ʿmạl ạ̹ydyk Я войду в Его врата с благодарностью 主早已预备 No sinful action/ Glenfinlas Би дахин боолчлогдохгүй Кетпечи, Ыйса, менден кетпечи Am fost născut în păcat ALLAHI KİM ARARSA Ajtódnál valaki megáll
Song not available - connect to internet to try again?