1) Yesu Ubangijinmu yana gun Uba yanzu, Yana shirya mana wurin zama can. Wata rana, wata sa'a, za ya dawo duniya, Za ya fyauce Masu Binsa nandanan. KORUS Muna jiran Sarkinmu, muna duban hanyarsa Ko da rana ya sauko, ko da dare ya iso, Sai ya iske mu da shirin karbarsa. 2) Kana daɗi za mu ji, za mu ga Ubangiji, Muna zamanmu tare har abada. Babu sauran ƃacin rai, farinciki ne kaɗai, Kullum murna za mu yi, ba fasawa. Korus 3) Ƴanuwa, ku zo yanzu, Yesu za ya wanke ku, Za ya kyauta muku rai har abada. Zo ku bi Mai Cetonku, faɗa masa laifinku, Shi ya shirya muku gafara tun dā. Korus无花果树已发嫩芽 ạ̉ḥbk rby yswʿ Иса Беним Достумдур Nitomany ny Mpamonjy Přijď k nám již, Duchu pravdy Залбирна hw ḥy ạ̉nt mlyknạ rwḥ ạllh nrḥb bk Con gioia
Song not available - connect to internet to try again?