1) Yesu ya zo da ƙaunarsa, Ya fanshe ni da jininsa, Ya cece ni da ikonsa, Yana riƙe da ni. KORUS Yesu ya ba da jininsa, Ya wanke dukan laifina, Ya kawo mini gafara. Ina yabon Yesu yanzu. 2) Tun da ya kira ni, na ƙi, Amma yanzu, Yesu zan bi, Ina misalin kyautarsa Da daɗin bautarsa! Korus 3) Yesu ya kawo gafara, Ya cika ni da Ruhunsa, Ya sake mini halina, Ubangijina ne. KorusMisollar Друг приди к Господу ныне Nek cela zemlja أدنو إليك أرتاح Калбымыз долы нурдан Tengo paz y alegría В Едем Muna Barka Dai da Zuwanku اسم يسوع قد حلا ʿywn ạlkl ttrjạk
Song not available - connect to internet to try again?