1) Yesu yana zuwa, lalle yana zuwa, Yesu yana zuwa duniyan nan. Za ya tara Masu Binsa daga ko'ina, Ku yi shiri domin zuwansa. KORUS Ku yi shiri, ku yi shiri! Ku yi shiri domin zuwansa Ku yi shiri, ku yi shiri Domin zuwansa. 2) Masu Binsa duka, Masu Binsa duka, Waɗanda su ke da shirinsu, Za a kai su Sama tare da Ubangiji Ku yi shiri domin zuwansa. Korus 3) Sai ku bar yin laifi, ku bar yin laifi, Sai ku bar yin laifi, Masu Bi. Babu sauran daman tuba ran da za ya zo, Ku yi shiri domin zuwansa. Korus 4) Sai mu yi addu'a, mu yi addu'a, Sai mu yi addu'a, Masu Bi, Don mu tarbe shi da murna ran da za ya zo, Mu yi shiri domin zuwansa. Korus 5) Sai mu yi ta aiki, mu yi ta aiki, Sai mu yi ta aiki, Masu Bi, Don mu kawo mutane dayawa gun Yesu Mu yi shiri domin zuwansa. KorusПок имон берди (анъанавий) Maqtanamız qúdiretli Qudayım! Улуқ Худа Po Tebe túžim viac Où trouver une retraite Ich weiß das mein Erlöser lebt Бар арманға жеткізіп Zdrav' buď, Kriste najmocnejší, zdravas' Vi vill ge Dig ära och tillbedjan يا صاحب الحنان
Song not available - connect to internet to try again?