1) Yesu, Ɗan Allah, Mai Ceto ne, shi za ya tsare ka. Yesu mai taimakonka ne, shi za ya tsare ka. KORUS Yesu zai tsare ka ko wane gu, ko wace sa'a. Yesu zai tsare ka, Yesu zai tsare ka. 2) Yesu ya mutu don laifinka, shi za ya tsare ka. Zunubai duka ya ɗauke su, shi za ya tsare ka. Korus 3) Yesu kuwa ya fito kabarin, shi za ya tsare ka. Shi ne mai rai har abada, shi za ya tsare ka. Korus 4) Idan jaraba ke damunka, Yesu zai tsare ka. Ikonsa ba za ya kare ba, Yesu zai tsare ka. Korus 5) Lokacin ciwo fa yana nan, shi za ya tsare ka. Shi ne mai warkarwa ba mai fi, shi za ya tsare ka. Korus 6) Kada ka ji tsoron kome dai, shi za ya tsare ka. Sama da duniya nasa ne, shi za ya tsare ka. KorusNebojte sa, nedeste sa Бүгдийг ав Ты для меня свет мира Залбирна عاجايىپ جەردى ٴتاڭىر سيلادى يوم ما قابلتك Numai Sfânta Carte la rugă m-a-ndemnat Билинмийор Таныг би ширтэн харъя Qudaı sózin berdi
Song not available - connect to internet to try again?