K : Yesu, Ɗan Allah, Mai Iko duka ne,
A : Yesu shi sarki ne, Sarkin Sarakuna.
A: Ya zo a duniya a cikin talauci,
A: Har suka yi shawara, suka giciye shi.
A: Ya zubda jinisa domina ya panshe mu.
A: Yesu ya ci nasara, nasara ta mutuwa.
A : Mu bi Yesu Mai Nasara da mutuwa.
A : Gama babu ceto sai wurin Yesu fa.
A: Yesu ya hau sama yana shirya wuri.
A: Lalle akwai murna ran da mun kai sama.
A: Yesu mun gode domin kai, ka tashi.
A: Taka ce har abada, har abada abadin.