1) Yesu Ɗan Allah ne, Mai Ceton duniya, Ya ƙaunace mu har ga mutuwa. Wanda ya ba da gaskiya gare shi Lalle ya tsira daga shari'a. KORUS Yesu mai iko duka ne, Ba za ya kasa ba daɗai, Sai mu kai bishara ko'ina a duniya Shi kuwa za ya taimake mu. 2) Ƴanuwanmu sun ƃata cikin duhu, Ba su da rai, ko sanin hanyarsa. Kada su mutu cikin zunubansu, Sai dai su zo su sami gafara. Korus 3) Ubangijinmu za ya sake zuwa Domin ya kai mu can a gidansa. Me za mu ce idan mun ƙi biyayya? Me za mu amsa masa ranan nan? Korus 4) Sauri, jama'a, Yesu yana kiran Duk Masu Bi su kama aikinsa. Maza da mata duk da yara kuma, Tashi, mu yi biyayya nandanan. KorusCroce Cross Croix Będziesz cieszyć się hyạ nhtf Biz jalǵyz júrmeımiz Haleluya, Pujilah Tuhanmu Шумит и бушует, кипит и клокочет Rab Sen çok sevdin رەبنى مەدھىيىلەڭلار Ježíš, Boží syn Aud şi azi cuvântul sfânt
Song not available - connect to internet to try again?